Posts

A dakatar da maganar zaɓen 'yar tinƙe a yanzu - Attahiru Jega

Image
  Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe ta INEC a Najeriya Farfesa Attahiru Jega ya faɗa wa Majalisar Dokoki cewa yin amfani da ƙarfin ikonsu wajen sanya wa sabuwar dokar zaɓen hannu "ba shi ne zaɓi mafi dacewa ba". Farfesa Jega ya bayyana haka ranar Lahadi yayin wani taron 'yan ƙasa kan Ƙudirin Dokar Zaɓe na 2021 wanda cibiyar Yiaga Africa ta shirya, inda ya nemi a dakatar da zaɓen 'yar tinƙe tukunna wanda dokar ta tanada. A cewarsa, Najeriya za ta fi samun natsuwa idan ta gudanar da zaɓe da sabuwar dokar zaɓe "saboda za ta kyautata ingancin zaɓukan da kuma shirye-shiyen gudanar da su". Ya ce: "Game da zaɓen 'yar tinƙe, tabbas harkokin zaɓe za su fi inganta idan muka yi amfani da 'yar tinƙe ta hanyar da ta dace. 'Yan majalisa sun sani cewa gwamnoni na yin yadda suke so da zaɓe ta hanyar wakilai saboda haka suka yi tunanin idan aka koma yin 'yar tinƙe za su samu 'yanci. "Sai dai ya kamata mu duba yanayin nan da kyau...hanya mafi sauƙi ba...

Mace ta kashe kanta a Kano

Image
  Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wata mata da ake zargin ta kashe kanta a unguwar Sheka da ke Ƙaramar Hukumar Kumbotso. 'Yan sandan dai sun ce matar ta kashe kanta ne ta hanyar amfani da wani fasasshen gilashin taga, inda ta yanka kanta bayan gartsa wa mahaifinta cizo sannan ta gutsire dan yatsanta da ke ciwo. A cewar dan uwan marigayiyar mai suna Muhammad Sanusi, kafin ‘yar uwar tasu ta kashe kanta ta yi fama da ciwon yatsa wato karkare, wanda har sai da ta kai ga sun rufe ta a ɗaki na tsawon kwana biyar, sakamakon yadda ta koma tamkar mai taɓin hankali. Ya ƙara da cewa a ranar da suka buɗe ta ne ta fasa gilashin tagar ɗakin da aka rufe ta sannan ta yanka kanta a makogoro. A shekarar 2021 an samu mutane sama da biyar da suka kashe kansu a Kano da ke arewacin Najeriya, wanda wasu daga cikinsu aka alaƙanta da matsalar ƙwaƙwalwa. Na baya-bayan da aka samu shi ne na wani matashi da ya kashe kan sa ta hanyar yanke al’aurar sa.

Afcon 2021: Salima Rhadia Mukansanga za ta zama macen farko da za ta yi rafli a Afcon

Image
  Salima Rhadia Mukansanga za ta kafa tarihin macen farko da za ta yi rafli a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Kamaru ke karbar bakunci. 'Yar kasar Rwandan, mai shekara 35 za ta busa wasa na karshe a rukunini na biyu ranar Talata tsakanin Zimbabwe da Guinea ranar Talata a filin wasa na Ahmadou Ahidjo da ke Yaounde. Guinea tana jan ragamar rukuni na biyu da maki hudu, bayan cin wasa daya da canjaras daya, ita kuwa Zimbabwe tana karshen teburi, bayan shan kashi a wasa biyu. Kuma karon farko da dukkan alkalai mata za su ja ragamar wasan Afcon tun lokacin da aka kirkiri gasar. Sauran matan sun hada da mataimakiya, Carine Atemzabong daga Kamaru da Fatiha Jermoumi daga Morocco da wadda za ta kula da VAR, Bouchra Karboubi daga Morocco. Ranar 10 ga watan Janairu, Mukansanga ta kafa tarihin macen farko da take cikin tawagar alkalai a karawa tsakanin Guinea da Malawi a matakin ta hudu mai jiran ko-ta-kwana a wasan da aka yi a Bafoussam.

An sace basarake a Filato

Image
 'Yan bindigaImage caption: 'Yan bindiga 'Yan bindiga sun sace wani basarake a jihar Filato. Basaraken Da Gyang Balak, yakasance mai fada aji a gundumar Vwang da ke karamar hukumar Jos ta Kudu. Dan Majalisar dake wakiltar karamar hukumar a majalisar dokokin jihar ne ya tabbatarwa da jaridar Punch labarin sace basaraken. An sace basaraken ne a ranar Lahadin data wuce da misalin karfe 8 na dare. Rahotanni sun ce an sace shi ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida a kan titin dake yankin Kuru. Lamarin ya faru ne kasa da wata guda bayan da wasu 'yan bindigar suka sace wani basarake a karamar hukumar Mangu wanda daga bisani suka sake shi bayan biyan kudin fansa.

Auren wuri 'yana karuwa a Najeriya'

Image
 Yara mataImage caption: Yara mata Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta ce auren wuri yana karuwa a Najeriya ne saboda gwamnatin tarayyar da gwamnatocin jihohi ba su dauki wata doka ta hana shi ba. A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta ce Najeriya ce kan gaba a nahiyar Afirka wajen aurar da yara mata da wuri. Kodayake dokar kare hakkin yara ta 2003 da gwamnatin tarayyar kasar ta yi ta haramta arar da yara 'yan kasa da shekara 18. Su kuwa jihohin kasar da ke amfani da tsarin shari'ar musulunci sun gaza amfani da dokar da gwamnatin tarayya ta yi a kan batu aurar da yara 'yan kasa da shekara 18. Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce," Abin damuwa ne ace kusan shekara 20 da zartar da doka a kasa, amma har yanzu ana aurar da yara mata 'yan kasa da shekara 18 a kasar".

Coronavirus: Yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya ya kai 250,929

Image
Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanan adadin mutanen da suka kamu da korona kullum a Najeriya, daga ƙididdigar hukumar NCDC. Muna sabunta shi ne da zarar an samu sabbin bayanai kullum. Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 301 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ranar Lahadi 16 ga watan Janairu 2022. Daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Legas tana kan gaba inda take da mutum 175 sai Ondo mai 42, sai Osun mai 23, sai Rivers 21 sai Nasarawa mai 16 sai kuma Oyo mai mutum 8. Sauran su ne Gombe da Kaduna inda kowacce daga cikinsu take da mutum 7. Akwai kuma sai babban birnin Najeriya Abuja da jihar kano ma su mutum 1 ga kowannensu. Yanzu dai adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta ya kai 250,929 amma an sallami mutum 224,052 daga asibiti. Yawan waɗanda suka rasa rayukansu sanadin cutar ta korona kuwa ya kai 3,103. Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauk...

'Kudin manyan attajirai 10 na duniya ya nunka a dalilin korona' - Oxfam

Image
 Jeff Bezos ya kashe yawancin kudin da ya mallaka ne a yawan shakatawa a sararin samaniya a kamfaninsa na Blue Origin Annobar korona ta kara azurta manyan attajiran duniya, amma a daya hannun annobar ta yi sanadin kara jefa mutane cikin talauci, kamar yadda kungiyar Oxfam mai fafutukar kare hakkokin jama'a ta ce. Ta ce karancin kudin shiga ga matalautan duniya ya janyo mutuwar mutum 21,000 a kowace rana, inji wani rahoton da ta fitar. Sai dai a daya hannun attajiran da suka fi kowa kudi na duniya sun nunka yawan kudin da suke da shi tun watan Maris din 2020 inji Oxfam. Oxfam na sakin rahoto kan rashin daidaito a duniya gabanin taron koli kan tattalin arziki da ake yi a Davos. Sai dai saboda annobar korona, a wannan shekarar ta biyu ba za a gayyaci mutnae su halarci taron ba kai tsaye, sai dai za a gudanar da shi ta intanet. Tattaunawar wannan makon zai hada da inda ake tsammanin annobar korona za ta nausa da duniya, da rashin daidaito kan yi wa al'umomin duniya riga-kafin cutar...

Asalin Maguzuwa da alakarsu da Hausa

Image
 Mutane da dama sun dade suna da wata tambaya a zuciyarsu a kan su waye Maguzawa? A wannan labarin BBC Hausa ta bayyana ko su waye Maguzawa kamar yadda wani marubuci kuma manazarci Ibrahim Aminu Daniya ya labarta mana. Su dai Maguzawa mutane ne Hausawa da yawancinsu manoma ne kuma suke a ƙauyukan ƙasar Hausa. Malam Ibrahim ya ce mutane ne masu ƙwazo da ƙoƙari, sai dai yawancinsu ba Addinin Musulunci suke bi ba, kamar wadanda suke tare da su a yankunan da suke, amma daga baya sannu a hankali wasu daga cikinsu na shiga Musulunci. Ya ƙara da cewa al'adunsu da yarensu, da kuma sutura sun dace da na Hausawa musamman kafin Jihadin Shehu Danfodio, kuma suna nan birjik a wurare da dama musamman kamar wasu ƙauyuka a ƙasar Kano da ma Katsina. Abin da aka fi karkata a kai na tarihi a cewar masanin shi ne mutane ne wadanda suka zo daga Habasha tun ana kiransu Majusu, suka riƙa sauya suna har aka dawo ana kiransu Maguzawa. Da yawan masu tarihi na ganin cewa su ne asalin Hausawa daga baya suka i...

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Navas, Van de Beek, Kurzawa, Dembele, Vlahovic, Tielemans, Carrol

Image
 Newcastle United na shirin aikawa da tayi kan golan Paris St-Germain Keylor Navas, sai dai kungiyar ta Faransa na son dan wasan mai shekara 35 dan kasar Costa Rica ya yi zamansa. (RMC Sport via Mail) Dan wasan tsakiya na Manchester United Donny van de Beek mai shekara 24 ya yi watsi da tayin komawa Newcastle saboda matsayinta na baya-baya da take kai a teburin Firimiyar Ingila. (Telegraph - subscription required) Newcaste din dai na kara samun nasara a kokarin da suke yi don dauko Diego Carlos, dan wasan Sevilla mai shekara 28. (Express) Chelsea na son daukan Layvin Kurzawa dan wasan baya na Paris St-Germain mai shekara 29 amma a matsayin na aro. (Fabrizio Romano on Twitter) Southhampton na tattaunawa da Chelsea kan sayen Armando Broja dan kasan Albania mai shekara 20. (Guardian) Dan wasan gaban Barcelona, Ousmane Dembele na iya komawa Manchester United ko Juventus ko Chelsea amma da alama Bayern Munichce ba ta da damar samun dan wasan mai shekara 24. (Sport - in Spanish) Leiceste...

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da harin fatattakar barayin daji a Neja

Image
 Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙaddamar wani gagarumin aikin sojoji a jihar Neja, wadda ke ci gaba da fuskantar hare-hare daga 'yan fashin daji da kuma gyauron 'yan ta-da-ƙayar-baya na Boko Haram da ta ce suna tserewa daga yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas. Mai magana da yawun shugaban ƙasar, Mallam Garba Shehu ya ce a wani umarni da ya bai wa hedikwatar tsaro kwanaki ƙalilan da suka wuce, Muhammadu Buhari ya buƙaci sojoji su mai da martani mai ƙarfi ga batutuwan kashe-kashe da sace mutane dona neman fansa a jihar ta Neja. A saƙonsa ga gwamnati da al'ummar Neja, Shugaba Buhari ya kuma jajenta musu kan matsalolin tsaro na baya-bayan nan da aka fuskanta. Mai magana da yawun shugaban Najeriyar, Mallam Garba Shehun, ya shaidawa BBC cewa manufar wannan da gagarumin aikin soja a jihar Nejan, shi ne matsalar tsaro da 'yan fashin na daga cikin dalilan da ya sa gwamnati ta dauki matakin. Malam Garba ya kara cewa: ''Bayanai sun nuna cewa 'yan fashin daji da ...

Ƴan bindiga sun sace mutum 15 a Jihar Neja

Image
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Neja ta tabbatar da sace mutum 15 a ƙauyen Kulho da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu. Jaridar Premium Times a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Wasiu Abiodun inda ya tabbatar da faruwar lamarin. Mista Abiodun ya bayyana cewa da misalin ƙarfe biyu na dare ne a ranar 14 ga watan Janairu wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka afka ƙauyen inda suka sace shanu ba iyaka. Ya bayyana cewa an tura dakarun ƴan sanda domin su ceto waɗanda aka sace. Jihar Neja na daga cikin jihohin Najeriya da ke fuskantar hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.  

Tinubu ya kai ziyara Jihar Katsina

Image
  Jagoran Jam'iyyar APC a Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara Jihar Katsina. Ƙungiyar da ke goyon bayan Tinubu ce ta wallafa hakan a shafinta na Facebook inda ta saka har bidiyonsa na ziyarar. Mista Tinubu ya tattauna da Gwamna Masari da kuma ƴan majalisar zartarwa ta jihar. Duk da dai babu ƙarin bayani kan abubuwan da suka tattauna amma ana ganin bai rasa nasaba da burin Tinubun na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023. Ko a makon nan sai da Tinubun ya kai ziyarar jaje zuwa Jihar Zamfara inda ya tallafa wa waɗanda harin ƴan bindiga ya ɗaiɗaita da naira miliyan 50.

Everton ta kori kocinta Rafael Benitez

Image
 Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Everton ta kori kocinta Rafael Benitez, ƙasa da wata bakwai da soma jagorantar ƙungiyar. Ƙungiyar ta naɗa Mista Benitez mai shekara 61 a matsayin kocinta a watan Yunin bara. Kafin ya zama kocin Everton, ya jagoranci ƙungiyar Liverpool da Real Madrid da Chelsea da wasu ƙanana da manyan ƙungiyoyi. A ranar Asabar ne Everton ta yi rashin nasara a wasanta da Norwich City da ci 2-1. Ƙungiyar ta ci wasa ɗaya kacal a wasanni 13 da ta buga a gasar Premier kuma ƙungiyar ta Everton ce ta 16 a bisa tebur inda saura maki shida kacal ta sauka ƙasan teburi. Ƙungiyar ta ce za ta bayar da sanarwa kan wanda zai maye gurbin Mista Benitez ba da jimawa ba.

Masu ikirarin jihadi sun kashe mutane da dama a Burkina Faso

Image
 Yan bindigar da ke ikirarin jihadi sun kashe mutane da dama a harin da suka kai a yankin Namssiguian da ke arewacin Burkina Faso. Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne ranar Asabar da safe wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum goma. Wakilin BBC a yankin ya ce ana sa ran adadin mutanen da suka mutu zai karu saboda har yanzu ba a gano mutane da dama ba. Kazalika mutane da dama sun jikkata yayin da kuma 'yan bindigar suka kona shaguna da gidajen jama'a. 'Yan sanda su ce 'yan bindigar sun kwashe sa'o'i da dama suna barna yayin da suka kai harin. A baya dai sun lalata turakun wayar tarho da zummar hana mutane kiran 'yan uwansu da ke wasu sasaan. Sojojin Burkina Faso na fafutukar kawar da masu ikirarin jihadi sai dai har yanzu wannan kokari nasu yana gamuwa da ckas. Hare-haren masu ikirarin jihadi sun yi sanadin mutuwar fiye da mutum 2,000 a cikin shekaru shida, yayin da fiye da mutum miliyan daya da rabi suka tsere daga gidajensu.

An kama wanda ake zargi da yi wa mata mai shekara 80 fyade a Nasarawa

Image
 Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wani mutum mai shekara 43 bisa zargin yi wa wata gyatuma mai shekara 80 a fyade. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Ramhan Nansel, ya fitar ranar Lahadi a Lafia, babban birnin jihar ce ta tabbatar da kama mutumin. A cewar sanarwar, a ranar 14 ga watan Janairun nan ne aka shigar da kara kan batun a ofishin 'yan sanda da ke Garaku, inda ake zargin mutumin, Dan’asabe Eddo, wanda da asalin jihar Kaduna ne amma yana zaune a kauyen na Garaku da ke karamar hukumar Garaku, Lokongo da haike wa tsohuwar. “An zarge shi da shiga gidan tsohuwar mai shekara 80, wacce take zaune ita kadai a wannan gida, sanna ya yi mata fyade.. “Bayan sun samu wannan labarin, 'yan sandan da ke ofishinmu na Garaku sun dauki mataki nan take inda suka kama mutumin da ake zargi." Sanarwar ta kara da cewa Kwamishina 'yan sandan jihar, CP Adesina Soyemi, ya bayar da umarni a kai batun sashen binciken masu aikata manya...

Buhari ya umarci sojojin Najerya su hanzarta gamawa da ƴan bindigar Neja

Image
  Shugaban Najerya Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin ƙasar su yi amfani da ƙarfi wajen murƙushe ƴan bindigar da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar. Cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce shugaban ya bayar da umarnin ne ga shalkatar ta Najriya. ''A matsayinsa na babban kwamandan sojojin Najeriya, shugaban ƙasa ya shirya wani gagarumin farmakin soji a jihar Neja wadda ke ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da ƴan Boko Haram da ke tserewa aga arewa maso yamma, da kuma arewa maso gabashin ƙasar nan'' in ji sanarwar. A sakonsa ga gwamnati da al’ummar jihar Neja kuwa shugaban ya ce “Ina so in miƙa saƙon ta’aziyya gareku, sakamakon matsalolin tsaro da suka faru a baya-bayan nan''. Ya ci gaba da cewa “A shirye gwamnatin tarayya take ta ƙarfafa goyon baya da hadin gwiwa da dukkan jihohin. Na yi imanin cewa tare da cikakken hadin kan ƴ...

NDLEA ta kama kwayar Tramadol miliyan 1.5 da za a kai Kano

Image
  Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama ƙwayar Tramadol miliyan daya da dubu dari biyar da za a kai jihohin Kano da Kebbi. An kama ƙwayoyin ne a filin jirgin saman Legas, da tashar jiragen ruwa ta Apapa. NDLA ta ce ta kuma gano wasu ƙwayoyi masu yawa da suka hadar da Diazepam, da Bromazepam, da allurar Pentazocine da suma aka so shigarwa jihar Kano Hukumar ta kuma ce ta kama makamai, da harsasai da dama daga wajen wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar Plateau. Ga bidiyon kayan da aka ƙwace nan a ƙasa don ku kalla.