'Kudin manyan attajirai 10 na duniya ya nunka a dalilin korona' - Oxfam
Jeff Bezos ya kashe yawancin kudin da ya mallaka ne a yawan shakatawa a sararin samaniya a kamfaninsa na Blue Origin
Annobar korona ta kara azurta manyan attajiran duniya, amma a daya hannun annobar ta yi sanadin kara jefa mutane cikin talauci, kamar yadda kungiyar Oxfam mai fafutukar kare hakkokin jama'a ta ce.
Ta ce karancin kudin shiga ga matalautan duniya ya janyo mutuwar mutum 21,000 a kowace rana, inji wani rahoton da ta fitar.
Sai dai a daya hannun attajiran da suka fi kowa kudi na duniya sun nunka yawan kudin da suke da shi tun watan Maris din 2020 inji Oxfam.
Oxfam na sakin rahoto kan rashin daidaito a duniya gabanin taron koli kan tattalin arziki da ake yi a Davos.
Sai dai saboda annobar korona, a wannan shekarar ta biyu ba za a gayyaci mutnae su halarci taron ba kai tsaye, sai dai za a gudanar da shi ta intanet.
Tattaunawar wannan makon zai hada da inda ake tsammanin annobar korona za ta nausa da duniya, da rashin daidaito kan yi wa al'umomin duniya riga-kafin cutar da samar da makamashi.
Alkaluman da mujallar Forbes ta wallafa na cewa a jumilla, kudin attajiran ya karu daga dala biliyan 700 zuwa dala tiriliyan 1.5, inda ta lissafa sunayen manyan attajirai 10 kamar haka: Elon Musk, Jeff Bezos, Iyalan gidan Bernard Arnault, Bill Gates, Larry Ellison, Larry Page, Sergey Brin, Mark Zuckerberg, Steve Ballmer da Warren Buffet.
Mujallar ta ce kudin da Mista Musk shi kadai ya mallaka ya nunka fie da sau kashi 1,000 cikin 100, inda na Mista Gates kuwa ya karu da kashi 30 cikin 100 kawai.
Oxfam ta ce wasu 'yan mata irin wadannan ba za su koma makaranta ba bayan annobar ta wuce
Oxfam ta kuma yi kira da a cire hakkin mallaka kan alluran riga-kafi domin sauran kasashen da ke fama da talauci su iya mallakar fasahar hada shi domin kowa ya amfana.
Comments