Buhari ya umarci sojojin Najerya su hanzarta gamawa da ƴan bindigar Neja
Shugaban Najerya Muhammadu Buhari ya bukaci sojojin ƙasar su yi amfani da ƙarfi wajen murƙushe ƴan bindigar da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a jihar Neja da ke tsakiyar ƙasar.
Cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kan harkokin watsa labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Lahadi, ya ce shugaban ya bayar da umarnin ne ga shalkatar ta Najriya.
''A matsayinsa na babban kwamandan sojojin Najeriya, shugaban ƙasa ya shirya wani gagarumin farmakin soji a jihar Neja wadda ke ci gaba da fuskantar hare-haren ‘yan bindiga da ƴan Boko Haram da ke tserewa aga arewa maso yamma, da kuma arewa maso gabashin ƙasar nan'' in ji sanarwar.
A sakonsa ga gwamnati da al’ummar jihar Neja kuwa shugaban ya ce “Ina so in miƙa saƙon ta’aziyya gareku, sakamakon matsalolin tsaro da suka faru a baya-bayan nan''.
Ya ci gaba da cewa “A shirye gwamnatin tarayya take ta ƙarfafa goyon baya da hadin gwiwa da dukkan jihohin. Na yi imanin cewa tare da cikakken hadin kan ƴan kasa, tabbas za mu shawo kan wannan matsala,” in ji shugaban kasar.
Comments