Afcon 2021: Salima Rhadia Mukansanga za ta zama macen farko da za ta yi rafli a Afcon


 Salima Rhadia Mukansanga za ta kafa tarihin macen farko da za ta yi rafli a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Kamaru ke karbar bakunci.

'Yar kasar Rwandan, mai shekara 35 za ta busa wasa na karshe a rukunini na biyu ranar Talata tsakanin Zimbabwe da Guinea ranar Talata a filin wasa na Ahmadou Ahidjo da ke Yaounde.

Guinea tana jan ragamar rukuni na biyu da maki hudu, bayan cin wasa daya da canjaras daya, ita kuwa Zimbabwe tana karshen teburi, bayan shan kashi a wasa biyu.

Kuma karon farko da dukkan alkalai mata za su ja ragamar wasan Afcon tun lokacin da aka kirkiri gasar.

Sauran matan sun hada da mataimakiya, Carine Atemzabong daga Kamaru da Fatiha Jermoumi daga Morocco da wadda za ta kula da VAR, Bouchra Karboubi daga Morocco.

Ranar 10 ga watan Janairu, Mukansanga ta kafa tarihin macen farko da take cikin tawagar alkalai a karawa tsakanin Guinea da Malawi a matakin ta hudu mai jiran ko-ta-kwana a wasan da aka yi a Bafoussam.

Comments

Popular posts from this blog

An kama wanda ake zargi da yi wa mata mai shekara 80 fyade a Nasarawa

Coronavirus: Yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya ya kai 250,929

An sace basarake a Filato