Masu ikirarin jihadi sun kashe mutane da dama a Burkina Faso


 Yan bindigar da ke ikirarin jihadi sun kashe mutane da dama a harin da suka kai a yankin Namssiguian da ke arewacin Burkina Faso.

Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne ranar Asabar da safe wanda ya yi sanadin mutuwar akalla mutum goma.

Wakilin BBC a yankin ya ce ana sa ran adadin mutanen da suka mutu zai karu saboda har yanzu ba a gano mutane da dama ba.

Kazalika mutane da dama sun jikkata yayin da kuma 'yan bindigar suka kona shaguna da gidajen jama'a.

'Yan sanda su ce 'yan bindigar sun kwashe sa'o'i da dama suna barna yayin da suka kai harin.

A baya dai sun lalata turakun wayar tarho da zummar hana mutane kiran 'yan uwansu da ke wasu sasaan.

Sojojin Burkina Faso na fafutukar kawar da masu ikirarin jihadi sai dai har yanzu wannan kokari nasu yana gamuwa da ckas.

Hare-haren masu ikirarin jihadi sun yi sanadin mutuwar fiye da mutum 2,000 a cikin shekaru shida, yayin da fiye da mutum miliyan daya da rabi suka tsere daga gidajensu.

Comments

Popular posts from this blog

An kama wanda ake zargi da yi wa mata mai shekara 80 fyade a Nasarawa

Coronavirus: Yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya ya kai 250,929

An sace basarake a Filato