Asalin Maguzuwa da alakarsu da Hausa
Mutane da dama sun dade suna da wata tambaya a zuciyarsu a kan su waye Maguzawa?
A wannan labarin BBC Hausa ta bayyana ko su waye Maguzawa kamar yadda wani marubuci kuma manazarci Ibrahim Aminu Daniya ya labarta mana.
Su dai Maguzawa mutane ne Hausawa da yawancinsu manoma ne kuma suke a ƙauyukan ƙasar Hausa.
Malam Ibrahim ya ce mutane ne masu ƙwazo da ƙoƙari, sai dai yawancinsu ba Addinin Musulunci suke bi ba, kamar wadanda suke tare da su a yankunan da suke, amma daga baya sannu a hankali wasu daga cikinsu na shiga Musulunci.
Ya ƙara da cewa al'adunsu da yarensu, da kuma sutura sun dace da na Hausawa musamman kafin Jihadin Shehu Danfodio, kuma suna nan birjik a wurare da dama musamman kamar wasu ƙauyuka a ƙasar Kano da ma Katsina.
Abin da aka fi karkata a kai na tarihi a cewar masanin shi ne mutane ne wadanda suka zo daga Habasha tun ana kiransu Majusu, suka riƙa sauya suna har aka dawo ana kiransu Maguzawa.
Da yawan masu tarihi na ganin cewa su ne asalin Hausawa daga baya suka ilimantu suka zama Hausawan da aka sani a yanzu.
To amma ya ce daga baya an samu kaulani, domin wasu na ganin cewa alama ta fi nuna cewa mutanen Afrika ta arewa ne, domin al'adar da ta fito daga nan irin tasu ce, kafin su dawo arewacin Afrika.
"Akwai mutanen da suka zo daga Habasha suka zauna a Dutsen Dala da ke Kano, kuma mashahurin sarkinsu shi ne Barbushe, wadannan mutane sun rika bautar gumaka, su kuwa Maguzawa da aka sani a yanzu ba sa bautar gumaka, amma suna da nasu abubuwan na tsaface-tsaface."
Har yanzu dai ba a san Maguzawa da wani harshe ba in ba Hausa ba.
Inda akafi samun su
Masanin ya ce an fi samun Maguzawa ne a kasar Hausa musamman ma a dazukan Kano da Katsina, akwai su suna nan amma sannu a hankali suna shiga cikin jama'a suna karbar Musulunci, don haka yanzu ƙalilan ne suka rage daga cikinsu.
Ya ce wasu daga cikin al'adunsu da suka yi kama da na Hausawan da suka rungumi Musulunci a yanzu sun hada da na bukukuwan aure ko na mutuwa da kaɗe-kaɗe da raye-raye.
"Sunayensu sun sha bambam da na Hausawan yanzu, domin su suna sanya sunaye ne dai-dai da yanayi ko lokaci.
Misali idan yanayin roron wake ne sai su ce 'Ci Wake,' ko idan lokacin damina ne sai su sa wa yaro suna 'Damina,' ko su sanya sunayen aljanu saboda su ne abokan mu'amalarsu musamman wajen bori da sauransu.
Marubucin ya ci gaba da cewa a yanzu dai babu wani ƙiyasi na yawan Maguzawan da suka rage a kasar Hausa, abin da kawai yake a fili shi ne yawansu ya ragu, kuma yana ci gaba da raguwa domin yawanci sun hade da sauran jama'a yadda in ba sun faɗa ba, ba za ka gane ba, don haka akwai yiwuwar watarana ma za su kare ɗungurungum.
Comments