Coronavirus: Yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya ya kai 250,929
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 301 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ranar Lahadi 16 ga watan Janairu 2022.
Daga cikin sabbin wadanda suka kamu jihar Legas tana kan gaba inda take da mutum 175 sai Ondo mai 42, sai Osun mai 23, sai Rivers 21 sai Nasarawa mai 16 sai kuma Oyo mai mutum 8.
Sauran su ne Gombe da Kaduna inda kowacce daga cikinsu take da mutum 7. Akwai kuma sai babban birnin Najeriya Abuja da jihar kano ma su mutum 1 ga kowannensu.
Yanzu dai adadin waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta ya kai 250,929 amma an sallami mutum 224,052 daga asibiti.
Yawan waɗanda suka rasa rayukansu sanadin cutar ta korona kuwa ya kai 3,103.
Hanyoyi 4 na kare kai daga cutar coronavirus
Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.
Yaya zan kare kaina daga cutar?
Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:
■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta
■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.
■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.
■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.
Comments