Everton ta kori kocinta Rafael Benitez
Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Everton ta kori kocinta Rafael Benitez, ƙasa da wata bakwai da soma jagorantar ƙungiyar.
Ƙungiyar ta naɗa Mista Benitez mai shekara 61 a matsayin kocinta a watan Yunin bara.
Kafin ya zama kocin Everton, ya jagoranci ƙungiyar Liverpool da Real Madrid da Chelsea da wasu ƙanana da manyan ƙungiyoyi.
A ranar Asabar ne Everton ta yi rashin nasara a wasanta da Norwich City da ci 2-1.
Ƙungiyar ta ci wasa ɗaya kacal a wasanni 13 da ta buga a gasar Premier kuma ƙungiyar ta Everton ce ta 16 a bisa tebur inda saura maki shida kacal ta sauka ƙasan teburi.
Ƙungiyar ta ce za ta bayar da sanarwa kan wanda zai maye gurbin Mista Benitez ba da jimawa ba.
Comments