Ƴan bindiga sun sace mutum 15 a Jihar Neja


Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Neja ta tabbatar da sace mutum 15 a ƙauyen Kulho da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu.
Jaridar Premium Times a Najeriya ta ruwaito mai magana da yawun ƴan sanda reshen jihar Wasiu Abiodun inda ya tabbatar da faruwar lamarin.
Mista Abiodun ya bayyana cewa da misalin ƙarfe biyu na dare ne a ranar 14 ga watan Janairu wasu da ake zargin ƴan bindiga ne suka afka ƙauyen inda suka sace shanu ba iyaka.
Ya bayyana cewa an tura dakarun ƴan sanda domin su ceto waɗanda aka sace.
Jihar Neja na daga cikin jihohin Najeriya da ke fuskantar hare-haren ƴan bindiga da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.


 

Comments

Popular posts from this blog

An kama wanda ake zargi da yi wa mata mai shekara 80 fyade a Nasarawa

Coronavirus: Yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya ya kai 250,929

An sace basarake a Filato