Tinubu ya kai ziyara Jihar Katsina
Jagoran Jam'iyyar APC a Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyara Jihar Katsina.
Ƙungiyar da ke goyon bayan Tinubu ce ta wallafa hakan a shafinta na Facebook inda ta saka har bidiyonsa na ziyarar.
Mista Tinubu ya tattauna da Gwamna Masari da kuma ƴan majalisar zartarwa ta jihar.
Duk da dai babu ƙarin bayani kan abubuwan da suka tattauna amma ana ganin bai rasa nasaba da burin Tinubun na tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023.
Ko a makon nan sai da Tinubun ya kai ziyarar jaje zuwa Jihar Zamfara inda ya tallafa wa waɗanda harin ƴan bindiga ya ɗaiɗaita da naira miliyan 50.
Comments