An kama wanda ake zargi da yi wa mata mai shekara 80 fyade a Nasarawa
Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wani mutum mai shekara 43 bisa zargin yi wa wata gyatuma mai shekara 80 a fyade.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Ramhan Nansel, ya fitar ranar Lahadi a Lafia, babban birnin jihar ce ta tabbatar da kama mutumin.
A cewar sanarwar, a ranar 14 ga watan Janairun nan ne aka shigar da kara kan batun a ofishin 'yan sanda da ke Garaku, inda ake zargin mutumin, Dan’asabe Eddo, wanda da asalin jihar Kaduna ne amma yana zaune a kauyen na Garaku da ke karamar hukumar Garaku, Lokongo da haike wa tsohuwar.
“An zarge shi da shiga gidan tsohuwar mai shekara 80, wacce take zaune ita kadai a wannan gida, sanna ya yi mata fyade..
“Bayan sun samu wannan labarin, 'yan sandan da ke ofishinmu na Garaku sun dauki mataki nan take inda suka kama mutumin da ake zargi."
Sanarwar ta kara da cewa Kwamishina 'yan sandan jihar, CP Adesina Soyemi, ya bayar da umarni a kai batun sashen binciken masu aikata manyan laifuka da ke Lafia domin gudanar da bcikakken bincike a kansa.
Comments