An sace basarake a Filato


 'Yan bindigaImage caption: 'Yan bindiga

'Yan bindiga sun sace wani basarake a jihar Filato.

Basaraken Da Gyang Balak, yakasance mai fada aji a gundumar Vwang da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.

Dan Majalisar dake wakiltar karamar hukumar a majalisar dokokin jihar ne ya tabbatarwa da jaridar Punch labarin sace basaraken.

An sace basaraken ne a ranar Lahadin data wuce da misalin karfe 8 na dare.

Rahotanni sun ce an sace shi ne a lokacin da ya ke kan hanyarsa ta komawa gida a kan titin dake yankin Kuru.

Lamarin ya faru ne kasa da wata guda bayan da wasu 'yan bindigar suka sace wani basarake a karamar hukumar Mangu wanda daga bisani suka sake shi bayan biyan kudin fansa.

Comments

Popular posts from this blog

An kama wanda ake zargi da yi wa mata mai shekara 80 fyade a Nasarawa

Coronavirus: Yawan mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya ya kai 250,929